6 Yuni 2025 - 19:20
Source: ABNA24
Amurka Ta Ƙara Sanya Sabbin Takunkumai Ga Iran

Ma'aikatar baitul malin Amurka ta bayyana sabbin takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran ga wa wasu mutane 10 da wasu hukumomi 27 sabbin takunkumai, daidai da manufar shugaba Donald Trump na matsa lamba kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlulbaiti AS - ABNA - A daidai lokacin da ake tattaunawa kan batun nukiliya, Kafofin yada labarai na kasa da kasa sun ruwaito cewa a ranar yau Juma'a a lokacin gida cewa ofishin kula da kadarorin ma'aikatar baitulmali ta Amurka ya kara mutane 10 da hukumomi 27 cikin jerin takunkumin da aka kakaba mata.

Hukumar yaki da tattalin arzikin Amurka da ke yaki da kasashen da ba su dace da manufofin siyasar Washington ba ta ce ta kakaba wa wasu Iraniyawa 9 da wani dan China daya takunkumi, sannan an kakaba wa wasu hukumomi 27 takunkumi na biyu a Iran, China, da UAE.

Takunkumin, wanda kuma ya shafi wasu hukumomi a Hadaddiyar Daular Larabawa da Hong Kong, na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Trump ke kokarin cimma sabuwar yarjejeniyar nukiliya da Tehran.

Your Comment

You are replying to: .
captcha